1 Corinthians 9

Hakkin Manzo

1Ba ni da ʼyanci ne? Ni ba manzo ba ne? Ni ban gan Yesu Ubangijinmu ba ne? Ba ku ne sakamakon aikina cikin Ubangiji ba? 2Ko da waɗansu ba su ɗauke ni a matsayin manzo ba, tabbatacce, ni manzo ne a gare ku! Gama ku ne hatimin manzancina a gaban Ubangiji.

3Wannan ita ce kāriyata ga waɗanda suke tuhumata game da manzancina. 4Ba mu da ʼyancin ci da sha ne? 5Ba mu da ʼyancin tafiya tare da matar da muka aura mai bi kamar sauran manzanni da ʼyanʼuwan Ubangiji da kuma Kefas suke yi? 6Ko ni da Barnabas ne kawai ba mu da ʼyanci a ɗauke mana aikin ci da kai?

7Wa yake ciyar da kansa yayinda yake aikin soja? Wa yake shukar gonar inabi, da ba ya cin amfaninta? Wa yake kiwon garke, da ba ya sha madararsa? 8Ina faɗin wannan bisa ga raʼayin mutum kawai ne? Ashe, Doka ma ba ta faɗa haka ba? 9Gama yana a rubuce a cikin Dokar Musa cewa, “Kada ka sa wa saniya takunkumi saʼad da yake sussukar hatsi.”
M Sh 25.4
Kuna tsammani a kan shanu ne Allah ya damu saʼad da ya ce haka?
10Babu shakka, ya yi maganan nan saboda mu ne. Ko ba haka ba? I, an rubuta wannan saboda mu ne, domin saʼad da mai noma yake noma, mai sussuka kuma yana sussuka, suna wannan ne da bege za su sami rabonsu daga girbin. 11In muka shuka iri na ruhaniya a cikinku, ashe, bai kamata mu yi girbin abin biyan bukatarmu daga gare ku ba? 12In waɗansu suna samun wannan taimako daga gare ku, ashe, mu ba mu fi cancanta mu samu ba?

Amma ba mu yi amfani da wannan ʼyancin ba. A maimakon haka, mun jure da kome, domin kada mu hana bisharar Kiristi yaɗuwa.
13Ashe, ba ku san cewa waɗanda suke hidima a haikali suna samun abincinsu daga haikali ba ne, waɗanda kuma suke hidima a bagade suna samun rabo a hadayar da suka miƙa ba ne? 14Haka ma Ubangiji ya umarta cewa ya kamata waɗanda suke waʼazin bishara, su sami abin biyan bukatarsu daga bisharar.

15Amma ban yi amfani da ko ɗaya daga cikin waɗannan ʼyancin ba. Ba kuma ina rubuta muku wannan da fata za ku yi mini waɗannan abubuwa ba ne. Gwamma in mutu, da wani yǎ hana ni wannan abin taƙama. 16Duk da haka, saʼad da ina waʼazin bishara, ba na taƙama, domin tilas ne a gare ni in yi waʼazi. Kaitona, in ban yi waʼazin bishara ba! 17In na yi waʼazi da yardar rai, ina da lada; in ba da yardar rai ba, ina dai cika amana da aka danƙa mini ne. 18To, mene ne ladana? Ladana kaɗai shi ne, in yi waʼazin bishara, in kuma yi shi a kyauta, yadda ba zan yi amfani da ʼyancina cikin waʼazin ba.

19Ko da yake ina da ʼyanci ba na kuma ƙarƙashin kowa, na mai da kaina bawa ga kowa, domin in rinjayi mutane da yawa. 20Ga Yahudawa na zama kamar Bayahude, domin in rinjayi Yahudawa. Ga waɗanda suke ƙarƙashin doka kuma, na zama kamar wanda yake ƙarƙashin Dokar, (ko da yake ni kaina ba na ƙarƙashin Doka), domin in rinjayi waɗanda suke ƙarƙashin Doka. 21Ga waɗanda ba su da Dokar kuwa, na zama kamar wanda ba shi da Dokar, (ko da yake ba ni da ʼyanci daga dokar Allah, amma ina ƙarƙashin dokar Kiristi), domin in rinjayi waɗanda ba su da dokar. 22Ga waɗanda ba su da ƙarfi, na zama marar ƙarfi, domin in rinjayi waɗanda ba su da ƙarfi. Na zama dukan abu ga dukan mutane, domin ko ta yaya in zai yiwu, in ceci waɗansu. 23Ina yin dukan waɗannan ne saboda bishara, domin in sami rabo a cikin albarkarta.

24Ba ku sani ba cewa a gasar gudu, dukan masu gudu sukan yi gudu, amma guda ne kaɗai yakan sami lada? To, sai ku yi gudu yadda za ku sami lada.

25Duk ʼyan wasan gasa sukan hori kansu sosai. Sukan yi haka domin su sami rawanin da ba zai daɗe ba. Amma mu muna yi ne domin mu sami rawanin da zai dawwama. 26To, ni fa ba gudu nake yi kamar mai gudu ba wurin zuwa ba. Dambena kuma ba naushin iska nake yi ba. 27Aʼa, ina horon jikina in mai da shi bawana, saboda bayan na yi wa waɗansu waʼazi, ni kaina kada in kāsa cancantar samun lada.

Copyright information for HauSRK